Ayuba 25:1-6

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

2“Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa; yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.

3Za a iya ƙirga rundunarsa? A kan wane ne ba ya haska haskensa?

4Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?

5In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa,

6mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”