Ayuba 35:1-16

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Sai Elihu ya ce,

2“Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’

3Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita, kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’

4“Zan so in ba ka amsa kai tare da abokanka.

5Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani; ku dubi gizagizai a samanku.

6In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah? In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa?

7In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku?

8Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai, adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai.

9“Mutane suna kuka don yawan zalunci; suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi.

10Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare,

11wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniya ya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’

12Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye.

13Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.

14Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara lokacin da kake cewa ba ka ganinsa, cewa ka kawo ƙara a wurinsa kuma dole ka jira shi.

15Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa ko kaɗan ba ya kula da mugunta.

16Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai; yana ta yawan magana ba tare da sani ba.”