Karin Magana 21:1-31
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so.
2Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke, amma Ubangiji yakan auna zuciya.
3Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
4Girmankai da fariya, su ne fitilar mugaye, wannan kuwa zunubi ne!
5Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.
6Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
7Rikicin mugaye zai yi gāba da su, gama sun ƙi su yi abin da yake daidai.
8Hanyar mai laifi karkatacciya ce, amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya.
9Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
10Mugun mutum yakan zaƙu ya aikata mugunta; maƙwabcinsa ba ya samun jinƙai daga gare shi.
11Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo; sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani.
12Mai Adalci kan lura da gidan mugu kan kuma zama sanadin lalacin mugu.
13In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.
14Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.
15Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci amma fargaba ga masu aikata mugunta.
16Mutumin da ya kauce daga hanyar fahimi kan zo ga hutu a ƙungiyar matattu.
17Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.
18Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya.
19Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.
20A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.
21Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa.
22Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai.
23Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.
24Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun.
25Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.
26Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.
27Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!
28Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka, kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada.
29Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi.
30Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji.
31Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.