Karin Magana 23:1-35

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka,

2ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai ci da yawa ne.

3Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi gama wannan abinci ruɗu ne.

4Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa.

5Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.

6Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi;

7gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai.

8Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza.

9Kada ka yi magana da wawa, gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a.

10Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā ko ka ɗiba gonar marayu,

11gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; zai kuwa yi magana dominsu.

12Ka mai da hankali ga umarni ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani.

13Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.

14Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa.

15Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, to, zuciyata za tă yi murna;

16cikin cikina zai yi farin ciki in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai.

17Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.

18Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.

19Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.

20Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci,

21gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

22Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.

23Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi.

24Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

25Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!

26Ɗana, ka ba ni zuciyarka bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,

27gama karuwa rami ne mai zurfi mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce.

28Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza.

29Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?

30Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.

31Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!

32A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.

33Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.

34Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa.

35Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?”