Zabura 100:1-5

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.

2Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

3Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

4Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

5Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.