Zabura 113:1-9
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji.
2Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma.
3Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji.
4Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai
5Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa,
6wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya?
7Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;
8ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu.
9Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.