Zabura 121:1-8

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo?

2Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.

3Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

4tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.

5Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;

6rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare.

7Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka;

8Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.