Zabura 124:1-8

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce,

2da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana,

3sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai;

4da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.

5Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.

6Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.

7Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira.

8Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.