Zabura 131:1-3
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
2Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
3Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.