Zabura 142:1-7
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji; na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.
2Na kawo gunagunina a gabansa; a gabansa na faɗa wahalata.
3Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina, kai ne wanda ya san hanyata. A hanyar da nake tafiya mutane sun kafa mini tarko.
4Duba ta damata ka gani; babu wanda ya kula da ni. Ba ni da mafaka; babu wanda ya kula da raina.
5Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Na ce, “Kai ne mafakata, rabona a ƙasar masu rai.”
6Ka saurari kukata, gama ina cikin matsananciyar bukata; ka cece ni daga waɗanda suke fafarata, gama sun fi ni ƙarfi sosai.
7Ka ’yantar da ni daga kurkuku, don in yabi sunanka. Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni saboda alherinka gare ni.