Zabura 149:1-9
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka.
2Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.
3Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.
4Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.
5Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.
6Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,
7don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane,
8don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,
9don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji.