Zabura 32:1-11
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Mai farin ciki ne shi wanda aka gafarta masa laifofinsa, wanda aka shafe zunubansa.
2Mai farin ciki ne mutumin da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.
3Sa’ad da na yi shiru, ƙasusuwana sun yi ta mutuwa cikin nishina dukan yini.
4Gama dare da rana hannunka yana da nauyi a kaina; an shanye ƙarfina ƙaf sai ka ce a zafin bazara. Sela
5Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina. Sela
6Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka yayinda kake samuwa; tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso, ba za su kai wurinsa ba.
7Kai ne wurin ɓuyata; za ka tsare ni daga wahala ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
8Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi; Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.
9Kada ka zama kamar doki ko doki, wanda ba su da azanci wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.
10Azaban mugu da yawa suke, amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.
11Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai; ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!