Zabura 34:1-22

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.

2Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.

3Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare.

4Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.

5Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

6Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa.

7Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.

8Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

9Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.

10Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa, amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.

11Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji.

12Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,

13ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.

14Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

15Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

16fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya.

17Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu.

18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

19Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

20yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.

21Mugunta zai kashe mugu; za a hukunta abokan gāban adalai.

22Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.