Zabura 6:1-10
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.
2Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
3Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?
4Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
5Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari?
6Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye.
7Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.
8Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.
9Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata.
10Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.