Zabura 72:1-20

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.

2Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.

3Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.

4Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.

5Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.

6Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.

7A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.

8Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.

9Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.

10Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.

11Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.

12Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.

13Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.

14Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.

15Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini.

16Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar; bari yă cika bisan tuddai. Bari ’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon; bari yă bazu kamar ciyayi a gona.

17Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.

18Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.

19Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa. Amin kuma Amin.

20Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.