Zabura 8:1-9
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.
2Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.
3Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,
4wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?
5Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
6Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,
7dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji,
8tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
9Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!