Zabura 131:1-3

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

Mawakin yana neman kwanciyar hali a Ubangiji. Ya kuma yi kira ga Isra'ila

Copyright (c) 2009, 2020 Biblica, Inc. CC BY-SA 4.0.

1Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina.

2Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.

3Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.