Zabura 150:1-6
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
Yabi Ubangiji a wurinsa mai tsarki. Yabe shi saboda ayyukansa masu iko
Copyright (c) 2009, 2020 Biblica, Inc. CC BY-SA 4.0.
1Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa.
2Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.
3Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo,
4yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
5yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai.
6Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.