Zabura 127:1-5
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza.
2Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
3’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi.
4Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.
5Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.