Zabura 128:1-6
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
2Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.
3Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.
4Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.
5Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,
6bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.