Zabura 129:1-8

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce,

2sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba.

3Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.

4Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.

5Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.

6Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma;

7da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.

8Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”