Zabura 20:1-9

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.

2Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.

3Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela

4Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.

5Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.

6Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa.

7Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.

8Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram.

9Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!