Zabura 21:1-13
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!
2Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela
3Ka marabce shi da yalwar albarka ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.
4Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin
5Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce; ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.
6Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.
7Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka ba zai jijjigu ba.
8Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka; hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.
9A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su.
10Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya, zuriyarsu kuma daga ’yan adam.
11Ko da yake suna shirya maka mugunta suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba;
12gama za ka sa su juye bayansu sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja.
13Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka; za mu rera mu kuma yabi ikonka.