Zabura 46:1-11

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

2Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

3ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

4Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.

5Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.

6Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.

7Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

8Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.

9Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.

10“Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.”

11Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela