Zabura 47:1-9

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.

2Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!

3Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.

4Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela

5Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.

6Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.

7Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi.

8Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.

9Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.