Zabura 63:1-11
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.
2Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
3Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.
4Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
5Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
6A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.
7Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
8Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.
9Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya.
10Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji.
11Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.