Zabura 64:1-10

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna; ka tsare raina daga barazanan abokin gāba.

2Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta.

3Sukan wāsa harsunansu kamar takuba su harba kalmominsu kamar kibiyoyi masu kisa.

4Sukan yin kwanto su harbi marar laifi; sukan yi harbi nan da nan, ba tsoro.

5Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu, sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu; su ce, “Wa zai gan su?”

6Sukan yi ƙulle-ƙullen rashin adalci su ce, “Mun gama ƙulla cikakkiyar maƙarƙashiya tsab!” Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa.

7Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi; nan da nan za a buge su su fāɗi.

8Zai juya harshensu a kansu yă kuma kawo su ga hallaka; duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a.

9Dukan mutane za su ji tsoro; za su yi shelar ayyukan Allah su kuma yi tunanin abin da ya aikata.

10Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangiji su kuma nemi mafaka a gare shi; bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi!