Zabura 66:1-20

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

2Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!

3Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke! Ikonka da girma yake har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.

4Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” Sela

5Ku zo ku ga abin da Allah ya yi, ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum!

6Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.

7Yana mulki har abada ta wurin ikonsa, idanunsa suna duban al’ummai, kada ’yan tawaye su tayar masa. Sela

8Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa;

9ya adana rayukanmu ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi.

10Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa.

11Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.

12Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.

13Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka,

14alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa sa’ad da nake cikin wahala.

15Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. Sela

16Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini.

17Na yi kuka gare shi da bakina; yabonsa yana a harshena.

18Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba;

19amma tabbatacce Allah ya saurara ya kuma ji muryata a cikin addu’a.

20Yabo ga Allah, wanda bai ƙi addu’ata ba ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni!