Zabura 80:1-19
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
1Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka
2a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu.
3Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.
4Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka?
5Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.
6Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a.
7Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu.
8Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.
9Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.
10Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.
11Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi.
12Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?
13Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa.
14Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi,
15saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka.
16An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.
17Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka.
18Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.
19Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.