Zabura 81:1-16

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!

2Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga, ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.

3Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata, da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;

4wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila, farilla ta Allah na Yaƙub.

5Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.

6Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku; an ’yantar da hannuwansu daga kwando.

7Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. Sela

8“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!

9Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku; ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.

10Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.

11“Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.

12Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu.

13“A ce mutanena za su saurare ni, a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,

14da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!

15Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.

16Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”