Zabura 82:1-8

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

1Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.

2“Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela

3Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

4Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

5“Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.

6“Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.

7Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”

8Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.