Zabura 133:1-3
Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)
Zabura 133: 'Yan'uwa suna zaman lafiya. Ubangiji ya albarkace su.
Copyright (c) 2009, 2020 Biblica, Inc. CC BY-SA 4.0.
1Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!
2Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai, yana gangarawa a gemu, yana gangarawa a gemun Haruna, har zuwa wuyan rigunansa.
3Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.