Zabura 134:1-3

Biblica Open Hausa Contemporary Bible (BSRK)

Yabon Ubangiji daga maibada. Albarka daga Ubangiji.

Copyright (c) 2009, 2020 Biblica, Inc. CC BY-SA 4.0.

1Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji.

2Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji.

3Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.